Рет қаралды 73
An gudanar da wani taron karawa juna sani a birnin Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, domin fadakarwa kan yadda al’adu da dabi’un Hausawa suke kokarin disashewa. Duk da karin karbuwa da harshen Hausa ke samu a fadin duniya, manazarta na cewa Hausawa suna ci gaba da banzatar da al’adu da dabi’unsu na kaka da kakanni. Baraka Bashir na dauke da rahoton.
Karin bayani akan VOA Hausa: www.voahausa.com
Karin bayani akan Facebook: / voahausa
Karin bayani akan Instagram: / voahausa
Karin bayani akan Twitter: / voahausa
Karin bayani akan Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci: bit.ly/3ElbQit
Shirye-shiryen Sashen Hausa na Muryam Amurka (VOA) wadanda suka hada da na rediyo, talabijin, shafin yanar gizo da kuma kafafen sada zumunta na Facebook, Instagram, Twitter da KZbin. Shirye-Shiryenmu sun hada da Taskar VOA da Labarun Mako da Dardumar VOA da Duniyar Amurka da kuma Lafiyarmu.
Sun kan kai ga mutum sama da miliyan 17 da ke bibiyar kafar a kasashen Najeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Chadi, Cote d’Ivoire da Jamhuriyar Benin. Sashen kan gabatar da labarai da dumi-duminsu, da batutuwan da suka shafi fashin baki, siyasa, kimiyya, fasahar zamani, kiwon lafiya, kasuwanci da nishadi tare da hadin gwiwar abokanan hulda na gidajen rediyo da talabijin sama da 100 a wasu yankunan Afirka.