Рет қаралды 1,468
Za a ji yadda ake gudanar da shirye-shiryen Kirismeti a yankin kudancin Najeriya.
Gwamnan Adamawa a Najeriya, ya rataba hannu kan dokar sabbin masarautu 7 a jihar Adamawa.
A Nijar, ma’aikatan kamfanin hakar zinariya, SML sun fara yajin aikin kwanaki biyar domin neman a biya musu bukatunsu.
Matakin da kotun kundin tsarin mulkin Mozambique ta yanke na tabbatar da nasarar Daniel Chapo na jam’iyyar FRELEMO a matsayin halastaccen shugaban kasa ya tada kura a kasar.
Yayin da ake shirin gudanar da sabon zabe a Jamus, babban kalubalen da ke gaban duk wanda ya samu nasara shi ne siyasar kasashen ketare.