Рет қаралды 1,100
Shugaban hukumar NMDPRA mai kula da dokokin fannin albarkatun man fetur da iskar gas, Injiniya Faruk Ahmed, ya bayyana cewa tun watan Febrairun shekarar 2022 ne ya kamata gwamnati ta janye tallafin man fetur saboda haka matakin cire tallafin da sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana na kan ka’ida.
Haka Zalika, hukumar NMDPRA tace a shirye take ta bada lasisi ga duk dan Najeriya dake da niyyar shigowa da man fetur cikin kasar don kawo sauki a samun wadataccen mai ga al’umma masu bukata.
Injiniya Faruk Ahmed ya bayyana hakan ne a Wata Hira ta musamman da murera Amurka a birnin tarayya Abuja yana mai yin kira ga yan Najeriya da kasa su shiga farga tare da mika bukatar dilallan man fetur su buda gidajen man su, su rika sayar da man saboda kamfanin NNPCL ya tabbatar da cewa akwai wadataccen mai da zai ishi yan kasa nan da tsawon wata guda.