Рет қаралды 15,980
Fitaccen Shugaban ‘yan bindiga Kachallah Bugaje ya tuba, ya mika wuya da kansa, ya kuma saki mutane (50) da ya yi garkuwa da su
Wani fitaccen shugaban ‘yan fashin daji, da aka fi sani da Kachallah Bugaje, ya yi watsi da ayyukan fashi da makami a bainar jama’a, ya kuma yi alkawarin mika wuya tare da mayakansa guda 50.
A cikin wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna 5 da dakika 42, wanda Zagazola Makama ya saki, Bugaje, wanda a yanzu yake son a yi masa lakabi da Zakiru Bugaje, ya yi tir da sace-sacen mutane da kashe-kashe, inda ya bayyana matakinsa na sauya wata sabuwar rayuwa.
“Mun yi garkuwa da mutane sama da 50, mun kira iyalansu, kuma mun nemi kudin fansa- wasu sun kai naira miliyan 10, wasu kuma naira miliyan 25. Amma daga baya mun sake su ba tare da mun anshi ko kwabo ba, saboda tsoron Allah.” Inji shi.
Bugaje ya nanata nadamar abin da ya aikata a baya, inda ya jaddada cewa ba zai sake shiga cikin aikata laifuka ba.
Ya yabi Annabi Muhammad (SAW) sannan ya bukaci sauran masu aikata miyagun laifuka da su yi watsi da wannan hanyar.