Wannan shi ke nuna mu 'yan Nigeria masaman Musulmai muna da kyakkyawan tarihi abun koyi, ba bature ba ne yaka wayantar da mu ya samemu da wayanmu ba bature ba ne yaka kawomana Adini ya samemu da adininmu, ba bature ba ne yaka kawomana cigaba ya samemu da cigabanmu,babbbature ba ne yaka kawomana tsari da mulki ya samemu da tsarinmu da mulkinmu, sai ya yaƙi kakaninmu ya kawomana ci baya a kowane fani har zuwa yanzu bature bai taɓa kawoma Nigeria abun da zata amfana ba ko guda ɗaya sai dai abun da shi ne zai amfana. Duk duniya babu Tsarin Mulkin da yakai tsarin Allah swa, turawa sun zo sun samemu muna a akan Tsarin Mulkin Adinin Musulumci,ya rabamu da shi,tun daka nan ya ɗaukarma kansa cewa ba zai taɓa bari mu zauna lafiya ba,kuma har yau har gobe turawa bazasu taɓa bari Nigeria ta zauna lafiya ba saboda zaman lafiyarmu asarar dukiyar ƙasarmu da yake samu ne, Kuma asarar rayukan turawan da ya rasa ne wajan kafa tsarinshi a Nigeria. Mu Kuma Musulmai saboda turawa sun shashantar da mu mun manta da duban jinanan kakaninmu da turawa suka kashe,mun manta da ƙyaƙyawan tsarin Allah swa da turawa suka rabamu da shi, mun manta da dukiyarmu da turawa ke ɗiba a Nigeria kullum kullum. Allah swa Ya ganar da mu ya bamu ikon komawa kyakkyawan tarihin da muka watsar