Рет қаралды 159,454
Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.
Shirin ya dawo ne bayan tafiya ɗan hutu sakamakon kullen annobar cutar korona.
A wannan kashi na 20, shirin ya tattauna da fitaccen tauraron fina-finan barkwanci na Hausa Sulaiman Bosho, inda ya amsa tambayoyin da za su sa ku dariya.
A cikin wannan hira mun tambayi Bosho ko an taɓa marinsa, sanna kuma ko zai yi wa matarsa kishiya. Kun san abin da ya ce? Sai kun kalli bidiyon har ƙarshe za ku ji.
Ɗaukar bidiyo da Gabatarwa: Yusuf Ibrahim Yakasai
Tacewa: Fatima Othman