Don allah ina bukatar wasu waqoqin shata mana a taimakeni dasu waqoqin sune yawan duniya mafarki a tafi a dawo alhajin musa malami karaye nagode shehu mai gidaje waqar sani audi da kuma waqarsa ta malam tijjani dagaxau??
@Shatane Жыл бұрын
Malam Abba wasu daga cikin wakokin da ka bukata mun riga mun sa su a wannan tashar, kamar wakar Sani Audi akwai ta a tashar nan, wakar yawon duniya mafarki ne kuwa wasu sun riga mu sa ta a KZbin saboda haka ba za mu iya sa ta ba domin kauce wa matsalar copyright. Wakar Tijjani Dagazau kuwa da mu ke da, cike ta ke da bakin zambo shi ne ya sa ba mu saka ta ba saboda doka ce da mu ka sa wa kan mu cewa ba za mu saka wakokin zambo da batanci a tashar nan ba amma duk sadda mu ka ci karo da wakar Tijjani Dagazau din wadda ba ta da zambo inshaAllahu za mu saka ma ku ita. Wakokin Musa Malami Karaye da Alhaji Shehu mai gidaje kuwa, ka biyo mu nan ba da dadewa ba za mu saka su a tashar nan. Mun gode kwarai.