Рет қаралды 10,831
A yayin da BBC Hausa ke cika shekara 65 da kafuwa ranar 13 ga watan Maris, sashen zai rika kawo muku hirarraki da tsofaffin ma'aikatansa.
Mun fara fitar da jerin hirarrakin ranar Talata 1 ga watan Maris na shekarar 2022.
Tsoffafin ma'aikatan sun yi bayanai ne a kan yadda suka samu aikin BBC da yadda ya kasance musu, da rayuwa bayan sun bar aikin da dai wasu abubuwan da suka shafe su.
A yau za mu gabatar muku da hira ne da tsohon shugaban sashen Hausa na BBC Mansur Liman, wanda a yanzu shi ne shugaban gidan rediyon tarayya na Najeriya FRCN.