Рет қаралды 16,333
Aliyu bakano ne a Najeriya wanda ya ke zaune a kasar Masira sannan ya shiga gasar kasidar larabci ta duniya mai taken Yariman Sha’iran Larabawa a birnin Abu Dhabi ta hadaddiyar daular larabawa. Ya tattauna damu game da rayuwarsa tsakanin Najeriya da Misira da kuma yadda aka yi ya sami shiga gasar larabawa a matsayinsa na bahaushe.